logo

HAUSA

An yi kira ga kasashen Afirka da su rungumi managartan dabarun rage tasirin sauyin yanayi

2022-10-27 10:52:59 CMG Hausa

Ministan muhalli, albarkatun daji da yawon shakatawa na kasar Namibia Pohamba Shifeta, ya yi kira ga kasashen Afirka, da su kafa ginshiki mai karfi, tare da aiwatar da matakai na hakika, a ayyukan wanzar da juriya da rage tasirin sauyin yanayi.

Mr. Shifeta, wanda ya yi wannan kira a jiya Laraba, yayin taron karawa juna sani kan sauyin yanayi da ci gaba, wanda ya gudana a birnin Windhoek, ya ce ya dace kasashen Afirka su dauki matakai masu tasiri, musamman a fannin aiwatar da isassun sabbin matakai, da amfani da kudade da ake iya hasashen tasirinsu wajen shawo kan kalubalen sauyin yanayi.

Ministan ya kara da cewa, duk da kokarin da kasashen Afirka suka yi wajen gabatar da gudummawar su ko NDCs, da kudaden gudanarwa, dabarun fasaha, da kwarewar masana na zama kalubale dake maida hannun agogo baya.

Mr. Shifeta ya ce "Duba da yanayin musamman na nahiyar Afirka, ya wajaba kasashen nahiyar su nemi a ba su kason kudade, da albarkatu na shawo kan tasirin sauyin yanayi, ciki har da musayar fasaha, da gina sanin makamar aiki, ta yadda nahiyar za ta cimma nasarar manufarta, ta rage fitar da iskar Carbon mai dumama yanayi, da gina juriyar tasirin sauyin yanayi.  (Saminu Alhassan)