logo

HAUSA

MDD: Ana fuskantar yiwuwar yankewar tallafin jin kai ga ’yan gudun hijirar yammacin Afirka

2022-10-27 10:52:19 CMG Hausa

Babban mai magana da yawun sakataren MDD Stephane Dujarric, ya ce karancin kudade na barazana ga tallafin da ya dace a samar ga akasarin jimillar ’yan gudun hijira 575,00 dake kasar Chadi, adadin da shi ne mafi yawa a yammacin Afirka.

Stephane Dujarric ya ce, mai yiwuwa karancin kudade ya tilasawa shirin abinci na MDD WFP, rage tallafin kusan mutum 300,000 cikin jimillar ’yan gudun hijirar Sudan, da jamhuriyar Afirka ta tsakiya, da Najeriya da Kamaru.

A cewar jami’in, ya zuwa watan Nuwamba mai zuwa, kaso 10 bisa dari na ’yan gudun hijirar ne kacal, shirin WFP zai iya baiwa tallafin abinci sakamakon karancin kudade. Bugu da kari, cikin jimillar ’yan gudun hijira 575,000 da aka tantance a watan da ya gabata, adadin ’yan kasar Chadi da suka rasa matsugunnansu ya ninka na baya, daga mutum 169,000 a shekarar 2020 zuwa 381,000 a 2022.

Kaza lika Dujarric ya ce a bana, kasar Chadi ta fuskanci ambaliyar ruwa mafi muni a ’yan shekarun baya bayan nan, bala’in da ya shafi sama da mutane miliyan 1. Ya ce domin tallafawa yunkurin gwamnatin kasar na tallafawa wadanda ibtila’in ya shafa, shirin abinci na duniya na samar da agajin abinci, da kudade ga iyalan da lamarin ya shafa.  (Saminu Alhassan)