logo

HAUSA

Ya Kamata Amurka Ta Soke Takunkumi Idan Tana Son Taimakawa Afirka

2022-10-26 20:12:59 CMG Hausa

Ranar 25 ga wata, rana ce ta yaki da takunkumi, wadda kungiyar SADC ta ayyana. Wasu kasashen Afirka sun sake yin kira ga Amurka da sauran kasashen yammacin duniya da su soke takunkumin da suke kakabawa kasar Zimbabwe.

Amurka ta dauki sama da shekaru 20 da sanyawa Zimbabwe takunkumi ya zuwa yanzu. Alkaluman kididdiga sun nuna cewa, Zimbabwe ta yi asarar dalar Amurka fiye da biliyan 40 sakamakon takunkumin da aka sanya mata baki daya. Hakika dai yadda Amurka ta kakabawa Zimbabwe takunkumi, ta nuna yadda ta dade tana tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasashen Afirka.

A watan Agustan bana, Antony Blinken, sakataren harkokin wajen Amurka ya ziyarci Afirka karo na 2, inda ya gabatar da sabbin tsare-tsaren Amurka kan yankin Afirka da ke kudu da hamadar Sahara. Amurka ta yi shelar cewa, nan da shekaru 5 masu zuwa, za ta kara azama kan yadda Afirka take bude kofa ga ketare, da taimakawa Afirka wajen tinkarar annobar cutar COVID-19 da farfado da tattalin arzikin Afirka. Amma akasarin ra’ayoyin jama’a na ganin cewa, a maimakon taimakawa ci gaban Afirka, Amurka ta yi amfani da Afirka domin samun moriya bisa manyan tsare-tsare, da sunan wai hada kai da Afirka.

Yanzu haka sakamakon tsanantar rikicin Ukraine, ya haifar da karuwar barazanar karancin abinci da makamashi, lamarin da ya kawo wa kasashen Afirka wadanda ke neman farfado da tattalin arzikinsu babban kalubale. Duk da haka Amurka da sauran kasashen yammacin duniya sun kau da kai daga matsalar da Afirka ke fuskanta wajen samun ci gaba, sun ci gaba da kara sanya takunkumi kan kasashe masu ruwa da tsaki, har ma sun tilasta wa kasashen Afirka ba su goyon baya.

Ko Amurka tana son taimakawa Afirka, ko kuma ba za ta cika alkawarinta kamar yadda ta yi a baya? Gaskiya ba ta buya. Kafin Amurka ta hada kai da Afirka, ya kamata ta soke takunkumin da take kakabawa wasu kasashen nahiyar.(Tasallah Yuan)