logo

HAUSA

Shugaban kasar Nijer ya ziyarci wurin gina madatsar ruwa ta Kandadji

2022-10-26 20:31:18 CMG Hausa

Shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum da ministocin makamashi, da tsaron kasa, da harkokin cikin gida da sauran wasu ministocin kasar, sun ziyarci wurin gina madatsar ruwa ta Kandadji tare da jakadan Sin dake kasar, Jiang Feng.

A yayin ziyarar ta safiyar jiya, shugaba Bazoum ya bayyana cewa, kasar Nijer ta gamsu da aikin gina madatsar ruwan, yana mai cewa kamfanin Sin mai aikin ginin ya shahara a duniya. A cewarsa, kamfanin na Sin ya tura kwararru zuwa wurin don sa kaimi da kyautata tsarin gudanar da aikin. Za a kammala gina madatsar ruwan ne a karshen shekarar 2025, inda Niger za ta ga cikar burinta.

A nasa bangare, jakada Jiang Feng ya bayyana cewa, Sin da Nijer sun kulla zumunci mai zurfi, kana Sin tana ba aikin ginin madatsar ruwan Kandadji muhimmanci, kuma za a ci gaba da sa kaimi ga aikin don tabbatar da gama shi akan lokaci, domin ba da gudummawa ga sha’anin samar da makamashi na kasar Nijer. (Zainab)