logo

HAUSA

Kasar Sin ba ta zama kalubale ko barazana

2022-10-26 19:40:01 CMG Hausa

 

Shugaban Amurka Joe Biden, ya tattauna da sabon firaministan Birtaniya Rishi Sunak, inda suka ce za su hada hannu wajen magance kalubalen kasar Sin.

Dangane da hakan, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau Laraba cewa, kasar Sin abokiyar hulda ce da kuma damar samun ci gaba ga dukkan kasashe amma ba kalubale ko barazana ba.

Ya ce kasar na kira ga Amurka, ta yi watsi da akidarta ta samun nasara daga faduwar wani bangare, ta kuma tafi tare da zamani. Ya ce maimakon yada tsohuwar akidarta ta “Sin barazana ce” da hada wata kungiya ba tare da wata kyakkyawar makoma ba, kamata ya yi ta yi kokarin samar da wani sabon tsari na bude kofa da tafiya tare da hadin gwiwar moriyar juna da gudanar da ayyuka a aikace, domin inganta zaman lafiya da ci gaba a duniya. (Fa’iza Mustapha)