logo

HAUSA

An Kaddamar Da Shirin Nuna Fina-finan Sin A Afrika

2022-10-26 21:20:52 CMG Hausa

A yau Laraba ne aka kaddamar da shirin nuna fina-finan kasar Sin a kasashen Afrika, inda ta hanyar kafofin yada labaru na Afirka da hukumomin kasar Sin masu ruwa da tsaki a Afirka, masu kallo a Afrika za su kalli fina-finai da shirye-shiryen Documentary kamar “The Pilot” da “Ten Years of Decoding” da “The Great Determintaion” cikin harsuna daban daban, wadanda suka bayyana kyakkyawan tsarin shugabancin kasar Sin na musamam a sabon zamani.

Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG da ma’aikatar kula da al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin ne suka kaddamar da shirin a kasa da kasa.

Shugaban CMG Shen Haixiong, ya bayyana cikin jawabinsa cewa, a watan Yunin bana, CMG ya kaddamar da shirin domin nunawa masu kallo a duniya kasar Sin a sabon zamani. Ya ce shirin da aka kaddamar a Afirka wanda shi ne irinsa na farko a nahiyar, wata alama ce ta nasarar hadin gwiwar kafafen yada labarai na kasar Sin da kasashen Afirka, da musayar al’adu tsakanin Sinawa da mutanen Afrika.

Ministan kula da yawon bude ido na Kamaru Bello Buba Maigari, ya ce shirin nuna fina-finan kasar Sin na kasa da kasa, wata dama ce ta inganta musayar al’adu tsakanin Sin da Afrika. Shirin ya ba matasan Afrika kwarin gwiwa da kyakkyawar fata. (Fa’iza)