logo

HAUSA

Ambaliyar ruwa ta halaka mutane 612 a Najeriya

2022-10-26 09:52:20 CMG Hausa

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa, mutane 612 ne suka gamu da ajalinsu, yayin da mutane miliyan 3 da dubu 219 da 780 ambaliyar ta yiwa mummunan barna a kasar, tun farkon daminar bana.

Ministar kula da harkokin jin kai da bala’u da jin dadin jama’a Sadiya Farouq ce ta tabbatar da hakan a Abuja, babban birnin kasar, a yayin wani taron manema labarai da aka shirya, don yiwa jama’a karin haske game da matakan da ma’aikatar da kuma hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar suka dauka kan yanayin ambaliyar ruwa a sassan kasar.

Ministar ta bayyana cewa, ya zuwa ranar Litinin, mutane miliyan 1 da dubu 427 da 370 ne ambaliyar ta raba da muhallansu, yayin da mutane dubu 2 da 776 a wasu sassan kasar suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Tana mai cewa, gidaje dubu 181 da 600 ne suka tabu kana wasu dubu123 da 807 kuma suka lalace baki daya.

A cewarta, eka dubu 176 da 852 na filayen noma ne suka tabu, yayin da eka dubu 392 da 399 kuma suka lalace baki daya. Ministar ta kuma tabbatar da rabon kayan agaji ga jihohi 21 na kasar da ambaliyar ta shafa, kuma tuni aka fara rabon abinci da sauran kayayyakin da ake bukata a wasu jihohin kasar.(Ibrahim)