logo

HAUSA

Kusoshin siyasa daga jam’iyyun siyasa na kasa da kasa sun taya Xi Jinping murnar zama babban sakataren kwamitin kolin JKS

2022-10-26 14:20:45 CMG Hausa

Jagororin siyasa daga kasashen duniya daban-daban, na ci gaba da buga waya ko aika da sakwanni don taya Xi Jinping murnar sake zabensa a matsayin babban sakataren kwamitin kolin JKS.

Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Seok-Youl ya bayyana cewa, yana farin ciki da aka sake zabar Xi Jinping a matsayin babban sakataren kwamitin kolin JKS. Ya ce, yana fatan kara yin mu’ammala da hadin gwiwa da shugaba Xi, domin wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a tsibirin Koriya da yankunan arewa maso gabashin Asiya. Kana yana fatan jamhuriyar jama’ar kasar Sin za ta samu wadata.

Shi ma shugaban Iran Seyed Ebrahim Raisi ya bayyana farin cikinsa da zaben Xi Jinping a matsayin babban sakataren kwamitin kolin JKS, yana fatan zai jagoranci jama’ar Sin don cimma sabbin manufofi masu cike da buri da samar da makoma mai haske.

Shugaban Aljeriya Abdelmadjid Tebboune ya bayyana cewa, jam’iyyar kwaminis ta Sin ita ce jagorar ci gaban da kasar Sin take samu a kowane lokaci. Kuma sake zaben Xi Jinping a matsayin babban sakataren kwamitin kolin JKS, yana kara tabbatar matsayinsa a cikin zukutan jama’ar kasar Sin.

Firaministan Abiy Ahmed Ali na kasar Habasha ya bayyana farin cikinsa ne, game da zaben da aka yiwa Xi Jinping a matsayin babban sakataren kwamitin kolin JKS. Mr. Abiy ya kara da cewa, a matsayinsa na managarcin shugaban JKS da jama’ar Sin, Xi Jinping ya samu jinjina daga al’ummar duniya. Yana kuma fatan karfafa mu’ammala da hadin gwiwa tsakanin jam'iyyar Prosperity na Habasha da JKS.

Bugu da kari, wasu manyan jami’an siyasa wadanda suka buga waya ko aiko wasiku sun hada da tsohon firaministan Iraki Allawi, shugaban jam'iyyar ’yancin kai da dimokuradiya ta Belarus Gedukevich, da tsohon shugaban Afirka ta Kudu Motlanti da sauransu. (Safiyah Ma)