logo

HAUSA

Kasar Sin ta kama tafarki na neman sabon ci gaba

2022-10-26 11:12:49 CMG Hausa

A karshen wannan makon ne, aka kammala babban taron wakilan JKS na 20, bayansa ne kuma babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, jagorancin sauran sabbin shugabannin don ganawa da manema labarai na cikin gida da na ketare. A jawanbin da ya gabatar, Xi ya bayyana cewa, babban taron wakilan JKS na karo na 20 da aka kammala, shi ne babban taro na kara daga tutar jam’iyyar, da hada karfi da karfe, da inganta hadin kai da kuma sadaukarwa.

Xi wanda aka sake zabarsa a matsayin babban sakataren jam’iyyar. Ya ce, ya kamata jam’iyyar ta yi wa jama’a aiki ta kuma dogara ga jama’a a kan tafiyar da aka sanya a gaba, da ci gaba da yin gyare-gyare da suka dace kan wannan tafiya da aka sanya a gaba. 

Yana mai cewa, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga kasashen ketare, da sa kaimi ga zurfafa yin gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga waje a dukkan fannoni. Kasar Sin mai wadata, za ta kara samar da damammaki ga duniya baki daya. Kuma kamar yadda kasar Sin ba za ta iya samun ci gaba ita kadai ba, haka ma duniya tana bukatar kasar Sin wajen samun bunkasuwarta.

Ya bayyana cewa, cikin shekaru sama da 40 na zurfafa gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta cimma wasu mu’ujiza guda biyu na saurin ci gaban tattalin arziki da zaman lafiyar al’umma na dogon lokaci.

Ya ce, tattalin arzikin kasar Sin yana da juriya da dama mai kyau, kuma tushensa mai karfi ba zai taba sauyawa ba, zai kuma ci gaba da kasancewa bisa yanayi mai kyau da inganci na dogon lokaci.

Ya kara da cewa, kasar Sin za ta yi aiki da sauran al’ummomin kasashe, don daukaka dabi’un bil-Adama na zaman lafiya, da bunkasuwa, da nuna adalci, da demikiradiya da ’yanci, da kiyaye zaman lafiya a duniya, da bunkasa ci gaban duniya, da ci gaba da gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)