logo

HAUSA

AU na goyon bayan tattaunawar zaman lafiya don kawo karshen rikicin a arewacin Habasha

2022-10-26 10:12:36 CMG Hausa

Kungiyar tarayyar Afirka (AU) ta shirya gudanar da tattaunawar zaman lafiya kai tsaye, tsakanin gwamnatin tarayyar Habasha da kungiyar ‘yan tawayen yankin Tigray(TPLF) a kasar Afirka ta Kudu.

Kungiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar jiya cewa, matakin wani bangare ne na shirin agazawa sassan dake rikici da juna a arewacin Habasha, don ganin an laluba mafitar siyasa ga rikicin dake faruwa a yankin Tigray na kasar Habasha.

Babban wakilin AU mai kula da yankin kahon Afirka, kana tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo, da tsohon shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, da kuma tsohuwar mataimakiyar shugabar Afirka ta Kudu Phumzile Mlabon-Ngcuka ne suka shirya tattaunawar.

Shugaban hukumar gudanarwar AU, Moussa Faki Mahamat ya bayyana cewa, ya samu kwarin gwiwa kan yadda sassan biyu suka fara nuna aniyar tabbatar da zaman lafiya da ma neman dawawwammen sulhu na siyasa a rikicin, bisa la’akari da muradun kasar.

Ya kara nanata aniyar kungiyar, na ci gaba da agazawa bangarorin, kamar yadda kasar ta tsara bisa jagorancin kungiyar, don ganin an kawo karshen amon bindigogi, a kokarin samar da kasar Habasha mai hadin kai da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma juriya.

A watan Agusta ne, rikici ya sake barkewa, inda gwmnatin Habasha ke zargin TPLF da sake tayar fada. Lamarin da ya kawo tsaiko ga kokarin kai kayayyakin agaji zuwa sassan arewacin kasar. (Ibrahim)