logo

HAUSA

Labarin wani dan kasar Afirka ta Kudu dake jin dadin rayuwa a kasar Sin

2022-10-25 14:25:50 CMG Hausa

Wani dan kasar Afirka ta Kudu mai suna Abrie ya zo kasar Sin ne saboda burinsa na zuwa “bangon duniya” don karo ilimi. Tun farko, ya yi shirin zama a nan na rabin shekara. Amma da rabin shekara ya cika, ya kara wani rabi, sai kuma shekara daya, shekara biyu, kawo yanzu ya shafe tsawon shekaru sama da hudu yana zaune a kasar Sin. Mene ne dalilin da ya sa malam Abrie ya zabi ya zauna a kasar Sin?

Abrie ya ce:

“Tun farkon farawa, na nemi wani aikin yi a birnin Shijiazhuang na kasar Sin, abokai na Sinawa sun ce Shijiazhuang karamin gari ne. Amma da na zo wajen, inaaaa! Ba karamin gari ba ne ko kadan!”

Birnin Shijiazhuang na lardin Hebei dake arewacin kasar Sin, zango na farko ne da Abrie ya yada a kasar Sin, kana wurin da ya fi dadewa a kasar. Kafin zuwan sa kasar Sin, Abrie ya taba ziyartar kasashe da yankuna da dama, ciki har da kasashen Afirka daban-daban, da Amurka, Birtaniya, New Zealand da sauransu. Ya ce ya riga ya fahimci kasashen yammacin duniya sosai, sauran sai kasashen dake gabashin duniya, don haka, ya zo nan kasar Sin, duk da cewa bai iya harshen Sin ba ko kadan. Abrie ya ce:

“Kasar Sin ta wuce abun da na yi zato kafin na zo. Sin kasa ce da ta dace a yi zauna cikinta, idan aka kwatanta da sauran wasu kasashe. Na farko, akwai tsaro sosai, na biyu, ana iya samun komai da komai, ba abun da ba za ka iya samu ba a nan. Sauran kuma, kudin ganin likita da kudin inshora, babu tsada kamar na sauran wasu kasashe da yankuna.”

A halin yanzu, Abrie yana aikin malanta a wata makarantar kasa da kasa dake birnin Kunshan na lardin Jiangsu dake gabashin kasar Sin, inda a yawancin lokuta ya kan yi mu’amala da yara. Idan ya samu lokacin hutu, yana sha’awar ziyartar kowane wuri a birnin Kunshan, har ma da sauran birane da garuruwan kasar Sin. Abrie ya ce, yanayin tsaro ba shi da kyau a kasarsa wato Afirka ta Kudu, don haka, cikakken yanayin tsaro a kasar Sin ya fi burge shi. Abrie ya ce:

“Har kullum a kan samu miyagun laifuffukan da ake aikatawa a kasar Afirka ta Kudu, ya fi kyau a zauna gida maimakom a fita waje da dare. Amma a kasar Sin, za ka iya fita waje a kowane lokaci. Da na dade da zama a nan, na gano cewa, babu wanda zai saci kayan ka idan ka fita waje da dare, za ka iya yarda da mutanen dake kewayen ka. Wannan shi ne dalili mafi muhimmnaci da ya sa na zabi ci gaba da rayuwa a kasar Sin.”

Bugu da kari, yadda mutanen kasar Sin ke son karbar baki shi ma ya burge malam Abrie kwarai da gaske. Ya ce wata rana ya fita waje da babur, amma babu caji, kuma bai san inda zai yi masa caji ba, sai wani Basine ya zo ya jagorance shi zuwa wurin cajin babur, har ya biya kudin cajin. Irin wannan abu ya baiwa Abrie mamaki sosai, kuma sannu a hankali, ya kulla zumunta tare da mutanen kasar Sin da yawa. Abrie ya ce:

“Farkon zuwa na kasar Sin, na ga mutane suna rawa a titi, gaskiya ya ba ni mamaki sosai! Yanzu ina ganin rayuwa a kasar Sin ya fi dadi idan aka kwatanta da sauran wasu kasashe da yankuna, musamman lokacin da nake mu’amala da mutanen kasar Sin, ina ganin suna da kirki sosai. Idan mun yi magana kan ‘ina kake zaune’, ‘kai dan asalin ina ne’, ko kuma ‘wane irin aiki kake yi’, za mu kara sabawa da juna.”

A kasar Afirka ta Kudu, akwai wani nau’in busasshen naman saniya da ake kira Biltong, wanda ke da dadi sosai. Abrie ya ce, idan ya samu lokacin hutu, ya kan samar da naman Biltong da kansa, har ma ya fara jan hankalin wasu mutanen kasar Sin da suke son dandana wannan abinci daga Afirka ta Kudu. Abrie ya ce, duba da yadda kasar Sin ke da ingantaccen tsarin jigilar kayayyaki, mutane daga sassa daban-daban na kasar, za su iya samun damar dandana naman Biltong da ya samar. Abrie ya ce:

“Aikewa da sakwanni a kasar Sin na da sauki sosai, kuma ba za’a kashe kudi da yawa ba. Idan aka aike da wani sako yau, za’a samu gobe a yawancin wurare. Amma na san ban da kasar Sin, aikewa da sakwanni a sauran wasu kasashe na da tsada sosai. Bugu da kari, sana’ar aikewa da sakwanni a nan na da inganci. Alal misali, idan na aike da sakwanni guda goma, tabbas za’a sami dukkansu. Amma idan a sauran wasu kasashe da yankuna ne, kila a samu matsaloli daban-daban, kamar wani sako ya bace, dayan sakon ya lalace, ko kuma an aike shi zuwa wani wuri na daban.”

A halin yanzu, samar da busasshen naman saniya na Biltong, wani abu ne da Abrie ke sha’awar ya yi bayan aiki. Amma saboda yadda kasar Sin ke kara habaka bude kofar ta ga kasashen ketare, ana kara samun mutanen da suke nuna sha’awa ga naman Biltong, al’amarin da ya wuce tsammanin Abrie, wato baya ga mutanen Afirka ta Kudu da suke aiki da rayuwa a kasar Sin, akwai mutane daga kasashen Turai da Amurka, har ma da mutanen kasar Sin da dama, da suke son naman Biltong. Abrie ya ce, yana tunanin ko zai iya maida sha’awar sa ta samar da naman Biltong, a matsayin wata sana’a, inda ya ce:

“A ganina, raya sana’o’i a kasar Sin ya fi sauki, idan aka kwatanta da kasa ta Afirka ta Kudu. A kasar Sin, akwai ingantattun muhimman ababen more rayuwar al’umma, kana mutanen kasar na son yin hadin-gwiwa da mu’amala, wato idan ka ce kana son yin wani abu, za ka iya farawa da samun ci gaba ba tare da wani jinkiri ba. Haka kuma, biyan kudi ta wayar salula ko ta kafar intanet, na samun karbuwa kwarai da gaske a kasar Sin, al’amarin da ya taimaka ga raya sana’o’i, musamman ga baki ‘yan kasashen waje. Ban da wannan kuma, wani abun da ya burge ni shi ne, kusan dukkan abubuwan da kake so, za ka iya samun su a kasar Sin, in dai ka yi kokari. Kamar na iya samun dukkan kayan girkin da nake bukata wajen yin naman Biltong.”

Kwanan nan malam Abrie mai shekaru 39 ya yi aure a kasar Sin, abun da ya kara ba shi kwarin-gwiwa wajen ci gaba da rayuwa a nan. Abrie ya bayyana cewa:

“Makomata ta na nan kasar Sin.” (Murtala Zhang)