logo

HAUSA

An bukaci kafafen watsa labaran Zimbabwe da su fallasa illar da takunkuman da kasashen yamma suka yiwa kasar

2022-10-25 10:23:01 CMG Hausa

Ministar watsa labarai da fadakar da jama’a ta Zimbabwe Monica Mutsvangwa, ta bukaci kafafen watsa labaran kasar, da su nuna adawa da takunkuman da kasashen yamma suka kakabawa kasar, tare da fallasa yadda takunkumai suka shafi ‘yan kasar.

Ta ce lokaci ya yi da ‘yan jaridun kasar, za su dakile farfagandar da kasashen yammacin duniya ke yadawa, wadanda ke neman haddasa rarrabuwar kawuna da rashin hadin kai a tsakanin ‘yan kasar.

Ministar tana magana ne, a yayin bude taron kungiyar raya kasashen kudancin Afirka (SADC) da aka gudanar a Harare, babban birnin kasar, wanda ya hallara ‘yan kasar da ‘yan jaridu, domin tattauna hanyoyin da za a bi wajen dakile illar da sashen watsa labaran ka iya shiga, sakamakon takunkuman fiye da shekaru ashirin da aka kakabawa kasar. (Ibrahim)