logo

HAUSA

Rundunar ’yan sanda a Najeriya ta yi gargadi game da barazanar tsaro a babban birnin kasar

2022-10-25 13:09:12 CMG Hausa

Rundanar ’yan sandan farin kaya a Najeriya, ta fitar da wani sabon gargadi, game da matsalar tsaro da ake fama da shi a Abuja, babban birnin kasar, inda ta yi kira ga jama’a da su yi taka tsan-tsan.

A cikin wata sanarwar da mai magana da yawun hukumar tsaron farin kaya wato DSS, peter Afunanya ya fitar, ya tunatar da cewa, a baya rundunar ’yan sandan farin kaya ta shawarci mazauna birnin Abuja, da su nutsu tare da kasancewa cikin shiri. Sai dai sanarwar baya-bayan nan na zuwa ne, bayan shawarwarin tsaro da ofishin jakadancin Amurka ya fitar a ranar Lahadi ga ma’aikatansa, game da yiwuwar kai harin ta’addanci a wuraren da jama’a ke taruwa a Abujan.

Ya kara da cewa, rundunar tana aiki da ragowar jami’an tsaro da masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da zaman lafiya a ciki da wajen Abuja. (Ibrahim Yaya)