logo

HAUSA

Za’a harba wani bangaren dakin gwaji mai suna Mengtian na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin

2022-10-25 15:38:39 CMG Hausa

A yau ne, aka kai mahadin wani bangaren dakin gwaji mai suna Mengtian na tashar binciken sararin samaniya da rokar Long March-5B Y4 da za’a yi amfani da ita wajen harba shi, zuwa yankin da za’a harba shi. Kuma nan bada jimawa ba za’a harba shi bayan da aka gudanar da bincike.

A halin yanzu, dukkan na’urorin da aka girka a filin harba taurarin dan-Adam dake birnin Wenchang na lardin Hainan dake kudancin kasar Sin, suna aiki yadda ya kamata, kuma sassan da suka halarci gwajin suna aiki tukuru, don tabbatar da gina tashar binciken sararin samaniya cikin nasara. (Murtala Zhang)