logo

HAUSA

Xi ya jaddada aiwatar da muhimman ka’idojin babban taron JKS a cikin rundunar sojojin kasar

2022-10-25 13:10:42 CMG Hausa

Babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping, ya umarci sojojin kasar da su yi nazari, da yada, da kuma aiwatar da ka’idojin jagorancin babban taron wakilan JKS karo na 20, da kara kaimi don cimma burin da aka sanya a gaba cika shekaru 100 da kafa rundunar ’yantar da jama’ar kasar Sin (PLS).

Xi, wanda har shi ne shugaban kasar Sin kana shugaban kwamitin kolin sojojin kasar, ya bayyana haka ne, lokacin da ya halarci taron manyan jami’an sojojin kasar.

Ya bayyana cewa, babban taron wakilan JKS karo na 20 da aka kammala, yana da babbar ma’ana ga yunkurin kasar na gina kasa ta zamani a dukkan fannoni mai bin tsarin gurguzu, da ciyar da kasar gaba daga dukkan fannoni. Bugu da kari, taron na da muhimmiyar ma’ana, a kokarin cimma burin da aka sanya gaba na cika shekaru 100 da kafa rundunar ’yantar da jama’a (PLA) da gina rundunonin soji da babu kamarsu a duniya baki daya.

Ya kuma jaddada cewa, ya kamata sojojin kasar su mayar da hankali wajen ganin sun cimma burinsu kafin a yi murnar cika shekaru 100 da kafuwar rundunar. Yana mai cewa, wannan shi ne babban aikin soja dake gabansu a cikin shekaru biyar din dake tafe. (Ibrahim Yaya)