logo

HAUSA

Ruwan sama kamar da bakin kwarya ya halaka mutane 195 a Nijar

2022-10-25 14:29:09 CMG Hausa

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta jamhuriyar Nijer ta sanar a jiya Litinin cewa, tun daga watan Yuni, ake ci gaba da sheka ruwan sama kamar da bakin kwarya a wasu sassan kasar, wanda ya haddasa mutuwar mutane 195.

Sanarwar ta ce, ruwan ya kuma haddasa nutsewar mutane baya ga gidaje da dama da suka rushe.

Ya zuwa jiya, mutane 195 sun mutu, wasu 211 kuma sun jikkata, kana fiye da dubu 320 sun yi fama da bala’in, kana an tabka hasara a bangaren sana’o’in kiwon dabbobi da noma.

A ranar 22 ga wata, firaministan jamhuriyar Nijer Ouhoumoudou Mahamadou ya bayyana a yayin taron tawagar shirya aikin gaggawa a lardin Diffa dake kudu maso gabashin kasar ind ake fama da bala’in, cewar gwamnatin ta tsara matakan tsugunar da wadanda lamarin ya shafa da kawar da cikas daga magudanar ruwa da gina madatsun ruwa da sauransu don kokarin tsaron rayukan jama’a a yankunan da bala’i ya shafa.

A kan shiga lokacin damina a jamhuriyar Nijer ne daga watan Yuli zuwa watan Satumba a duk shekara. A shekarar 2021, ambaliyar ruwa a kasar Nijer ta haddasa mutuwar mutane 77, kana fiye da dubu 250 sun yi fama da bala’i. (Safiyah Ma)