logo

HAUSA

Yan majalisar dokokin Sin za su yi muhawara kan daftarin dokokin da za a yiwa gyare-gyare

2022-10-25 14:15:53 CMG Hausa

A wannan makon ne ‘yan majalisar dokoki na kasar Sin, za su tattauna kan daftarin gyare-gyare ga dokokin kasar, matakin dake nuna karfin kafa dokoki da sanya ido kan kundin tsarin mulki.

Mai magana da yawun hukumar kula da harkokin majalisar dokoki ta zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zang Tiewei, ya bayyana cewa, manufar daftarin gyare-gyaren, ita ce kyautata tsari da samar da kyakkyawan hadin kai tsakanin shawarwarin da ‘yan majalisar suka gabatar da yin gyare-gyare.

Zang ya bayyana cewa, gobe Laraba ne za a mikawa wani zama na zaunannen kwamitin NPC daftarin kwaskwarimar don yi masa karatu na farko.

Bugu da kari, matakin zai inganta tsarin dokoki da aikin majalisa da zaunannen kwamitinta, da kara abubuwan da suka dace don biyan bukatun sake fasalin tsari na sanya ido, da ma inganta abubuwan da suka dace na dokoki da ka’idoji na dokokin cikin gida da kara sake nazartar takardun da aka saba bisa al’ada. (Ibrahim)