logo

HAUSA

Cinikayyar Waje Na Kasar Sin Ya Karu Da Kaso 9.9 A Watan Janairu Zuwa Satumba

2022-10-24 19:33:43 CMG Hausa

lkaluman hukuma na nuna cewa, cinikayyar kayayyaki na ketare na kasar Sin, a cikin watanni 9 na farkon shekarar 2022 da muke ciki, ya karu da kashi 9.9 cikin 100, zuwa kudin Sin RMB Yuan triliyan 31.11, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 4.75.

A cewar babbar hukumar kwastan ta kasar Sin, darajar kayayyakin da kasar Sin take fitarwa zuwa ketare, ta karu da kashi 13.8 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara, zuwa Yuan triliyan 17.67, yayin da darajar kayayyakin da ake shigo da su cikin kasar daga ketare, ta karu da kashi 5.2 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara, zuwa Yuan triliyan 13.44.

Daga watan Janairu zuwa Satumba, cinikayyar kasar Sin da kungiyar kasashen kudu maso gabashin Asiya wato ASEAN, da kungiyar tarayyar Turai wato EU, da kasar Amurka, ta karu da kashi 15.2 cikin 100, da kashi 9 cikin 100 da kuma kashi 8 cikin 100 bi da bi.

A cikin wannan wa’adi, cinikayyar kasar Sin da kasashen dake aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, ya karu da kashi 20.7 cikin 100 kan makamancin lokaci na bara, zuwa Yuan triliyan 10.04. (Ibrahim)