logo

HAUSA

Samun ci gaba mai inganci babban aiki ne na zamanantar da kasa mai bin salon tsarin gurguzu

2022-10-24 14:11:54 CMG Hausa

A yau Litinin ne mataimakin darektan ofishin kula da kwaskwarima na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma mataimakin darektan hukumar kula da kwaskwarima da raya kasa ta kasar Mu Hong ya bayyana cewa, rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, ya mayar da samun ci gaba mai inganci a matsayin babban aiki na zamanantar da kasa mai bin salon gurguza daga duk fannoni, lamarin da ya sake shaida cewa, ingancin samun ci gaba yana da ma’ana matuka.

Mu Hong ya fadi hakan ne a yayin taron ganawa da manema labarai da aka shirya, domin kara fahimtar rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20, inda ya yi nuni da cewa, rahoton ya tsara manufofi a bangarori shida bisa manyan tsare-tsare kan batun, game da yadda za a ingiza ci gaba mai inganci, wadanda ke hada hanzarta aikin tsara ayyukan raya kasa, da tabbatar da manufar raya kasa ta hanyar yin kirkire-kirkire, da kafa tsarin tattalin arzikin kasuwar tsarin gurguza mai inganci, da farfado da kauyuka daga duk fannoni a fadin kasar, da ciyar da yankunan kasa gaba yadda ya kamata, da kara bude kofa ga ketare.

Jami’in ya kara da cewa, manufofin za su kara imanin al’ummomin kasa da kasa kan ci gaban kasar Sin. (Jamila)