logo

HAUSA

Ana bukatar dogon lokaci yayin tabbatar da wadata a fadin kasar Sin

2022-10-24 14:39:57 CMG Hausa

A yau Litinin ne darektan ofishin nazarin manufofin raya kasa na kwamitin kolin JKS Jiang Jinquan, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labarai da aka shirya, domin kara fahimtar rahoton babban taron wakilan JKS karo na 20 cewa, cimma burin tabbatar da wadata a fadin kasa, aiki ne da ake yi cikin dogon lokaci, kuma ya dace a gudanar da shi bisa matakai daban daban.

Jami’in ya kara da cewa, dalilin haka shi ne, hakikanin yanayin da kasar Sin ke ciki, wato har yanzu kasar Sin kasa ce mai tasowa, kamata ya yi a rika tattara dukiyoyin zamantakewar al’ummun kasar, domin daga matsayin rayuwar al’ummun kasar, kuma ya dace a yi kokari bisa matakai daban daban, ta yadda al’ummun kasar za su ga sauyi daga sakamakon da aka samu. (Jamila)