An Zabi Xi Jinping A Matsayin Babban Sakataren Kwamitin Kolin JKS
2022-10-23 13:26:41 CMG Hausa
An zabi Xi Jinping, a matsayin babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20, yayin zaman farko na kwamitin da ya gudana Lahadin nan, kamar yadda aka bayyana cikin wata sanarwar bayan taron.
Zaman wanda Xi ya jagoranta, ya samu halartar mambobi 203 na kwamitin kolin JKS na karo na 20 da kuma mambobi masu jiran gadon wani mukami 168.
Haka kuma a yayin wannan zama, an bayyana Xi a matsayin shugaban hukumar kolin sojojin kwamitin kolin JKS.
Mambobin zaunannen kwamitin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS da aka zaba a zaman taron, sun hada da Xi Jinping, da Li Qiang, da Zhao Leji, da Wang Huning, da Cai Qi, da Ding Xuexiang, da Li Xi.
Bugu da kari, a yayin taron, an zabo mambobin ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, wanda kuma ya amince da mambobin sakatariyar kwamitin kolin JKS da zaunannen kwamitin hukumar siyasa na kwamitin kolin JKS ya gabatar.
Zaman taron ya kuma sanar da sunayen mambobin kwamitin soja na kwamitin tsakiya na JKS.
Haka kuma zaman ya amince da sakatare da mataimakan sakatarori da mambobin zaunannen kwamitin hukumar ladabtarwa wato CCDI ta kwamitin kolin JKS, da aka zaba a yayin cikakken zama na farko na hukumar CCDI karo na 20. (Ibrahim)