logo

HAUSA

An zartas da kuduri kan "gyararren kundin ka'idojin JKS"

2022-10-23 14:20:06 CMG Hausa

An zartas da kuduri game da kundin ka'idojin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin da aka gyara, a yayin babban taron wakilan Jam’iyyar Kwaminis na kasar Sin karo na 20 da aka kammala jiya, inda aka amince da shigar da sabbin ci gaban tunanin shugaba Xi Jinping game da tsarin gurguzu mai halayyar musamman ta kasar Sin a sabon zamani da ake ciki, bayan babban taron wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 19 a cikin kundin ka’idojin Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin.

An kuma tabbatar da babban burin raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar Sin, wato za a cimma nasarar zamanintar da kasar Sin mai bin tsarin gurguzu nan da shekarar 2035, da gina kasar Sin ta yadda za ta zama kasa mai karfi dake bin tsarin gurguzu na zamani nan zuwa tsakiyar wannan karni, wato yayin cika shekaru 100 da kafa jamhuriyar Jama’ar kasar Sin.

Taron ya amince da shigar da aikin sa kaimi ga farfado da al’ummar kasar Sin ta hanyar zamanintar da kasa bisa tsarin kasar Sin da aka gabatar a gun taron wakilan JKS karo na 20 a cikin gyararren kundin ka’idojin JKS.

Haka kuma, taron ya amince da shigar da cikakken tsarin demokuradiyya da ake damawa da jama'a, da kafa tsarin kyautata yin zabe, da shawarwari, da gabatar da kuduri, da tafiyar da harkoki, da sa ido bisa tsarin demokuradiyya a cikin kundin ka’idojin JKS da aka gyara.

Taron ya amince da shigar da tabbatar da manufar “kasa daya amma tsarin mulki biyu” da nuna adawa da hana neman ‘yancin kan Taiwan a cikin kundin.

Kana taron ya amince da shigar da ra’ayin martaba halayen dan Adam na samun zaman lafiya, da ci gaba, da adalci, da demokuradiyya, da ‘yanci, da sa kaimi ga shimfida duniya mai zaman lafiya da tsaro da wadata da bude kofa da kiyaye muhalli na dogon lokaci a cikin kundin.

Hakazalika game da raya Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, taron ya amince da shigar da aikin martaba ka’idojin jam’iyyar da sa ido ga membobin jam’iyyar a dukkan fannoni, da tabbatar da jami’ai ba su yi amfani da mukamansu ko damar da suke da ita har ma su yi tunanin karbar cin hanci cikin kundin. (Zainab)