logo

HAUSA

Shin za a samu barkewar cutar kyandar biri a duk fadin duniya?

2022-10-23 18:09:15 CMG Hausa

Tun bayan watan Mayu na shekarar da muke ciki, cutar kyandar biri ta barke a wasu kasashen Turai da Amurka ba zato ba tsammani, sa’an nan cutar ta yadu a sassa daban daban na duniya. Babban darektan hukumar kiwon lafiya ta kasa da kasa wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya sanar a ranar 23 ga watan Yuli cewa, barkewar cutar kyandar biri ta kasance lamarin ba zata da ya shafi lafiyar al’umma, wanda ya kamata kasashen duniya su mai da hankali a kai. Ana kara samun masu kamuwa da cutar wadanda ba su taba zuwa wuraren da aka samu barkewar cutar ba. Hukumar WHO ta nuna cewa, a wasu kasashen da ba a samu barkewar cutar ba, an gano masu kamuwa da cutar wadanda ba su taba zuwa wuraren da aka taba samun barkewar cutar ba. Hakan ba safai ya kan faru ba. Yanzu ana kokarin nazarin asalin cutar.

To, ko hakan ya nuna cewa, cutar ta kyandar biri ta fi kama mutane? Michael Ryan, darektan zartaswa mai kula da ayyukan gaggawa na WHO ya bayyana wa manema labaru cewa, a shekaru da dama da suka wuce, yaduwar cutar kyandar biri ta samu sauye-sauye, barkewar cutar ta fadada a duniya. A yankin yammacin Afirka da yankin Sahel, sakamakon sauyin yanayi, ya sa mutane da namun daji rasa abin da za su yi, sai suka sauya salon rayuwarsu ta yadda za ta dace da yanayin, watakila hakan ya kawo kusanci sosai tsakanin namun daji da mutane. A wani lokaci, mutane da namun daji suna takara da juna domin samun abinci. Ya zama tilas a kara sanin muhalli da aikace-aikacen mutane a yankuna masu ruwa da tsaki baki daya, ta yadda za a iya dakile yaduwar cutar ta kyandar biri daga dabbobi zuwa bil Adama daga tushe.

Masana masu ruwa da tsaki sun yi nuni da cewa, mai yiwuwa karuwar masu kamuwa da cutar kyandar biri tana da nasaba da kau da cutar agana baki daya tsakanin mutane. Tun bayan shekarar 1980, ba a yi wa mutane alluran rigakafin cutar ta agana ba, mutane ba za su iya yaki da cutar kyandar biri kamar yadda suka yi a baya ba. A shekaru 40 da suka gabata, yawan masu kamuwa da cutar kyandar biri a kasar Kongo (Kinshasa) ya karu sama da sau 14, wato daga mutum daya a cikin ko wadanne mutane dubu 10, zuwa mutane 14 a cikin ko wadanne mutane dubu 10.

Wani abun mamaki na daban shi ne, mutane da yawa da suka kamu da cutar kyandar biri a kwanan baya, ‘yan luwadi ne, wadanda suke kaunar mata da maza duka, ko mazan da suka sadu da maza. Dangane da lamarin, masana sun yi bayani da cewa, ya zuwa yanzu ba a tabbatar da ko cutar kyandar biri tana yaduwa a tsakanin mutane ne kamar yadda cutar AIDS take yaduwa tsakanin mutane ta hanyar jima’i ba.(Tasallah Yuan)