logo

HAUSA

Yarinyar dake neman cimma mafarkin rigar Han, da nufin sanya mutane mafi yawa suke sha’awa kan al'adun gargajiyar kasar Sin

2022-10-24 19:23:58 CRI

Rigar Han, wani nau’in kayan sutura na gargajiya ne na kabilar Han ta kasar Sin, wadda ta bullo a kimanin shekaru dubu biyar da suka gabata. A halin yanzu, rigar Han na kara samun karbuwa a yankuna daban daban na kasar, musamman ma a wasu shahararrun wuraren yawon shakatawa, Sinawa da yawa na saka rigar Han. Wasu mutane na son sanya rigar Han ne domin yanayin ta mai kyau, wasu kuma saboda sha'awar al'adu masu ma’ana da ke tattare da ita.

Ga Shu Qiuhong, rigar Han riga ce ta yau da kullum, wadda take sakawa a lokacin da take zuwa sayen abinci, da kuma zuwa sayayya.

Tun da farko, tana son sanya rigar Han ne kawai, kuma ta yi bincike kan yadda ake daidaita tufafin, daga baya, a hankali ta duba bayyanai dangane da rigar Han, daga nan ta fara sha'awar nazarin al'adun gargajiyar kasar Sin. Shu Qiuhong tana jin cewa, ta sami burin da take fatan cimmawa a rayuwa, kana tana son yada ma'ana da al'adun tufafin gargajiya ga mutane da yawa, tare da canza tunanin wasu mutane game da rigar Han.

A kan titin da ba shi da nisa da tafkin Daming, wato wani shahararren wurin yawon shakatawa dake birnin Ji’nan dake gabashin kasar Sin, Shu Qiuhong tana gudanar da wani shagon rigar Han mai girman murabba'in mita 30 zuwa 40. Duk da cewa karamin shago ne, amma yana da wani salo na musamman. Rigunan Han masu kala-kala, kayan kwalliyar gashi masu kyau, da takalman sawaye salo iri-iri, suna sa duk wanda ke shiga cikin wannan shagon, ya ji kamar ya dawo lokacin can-can-can da.

An haifi Shu Qiuhong a wani kauyen dake lardin Guizhou a kudu maso yammacin kasar Sin, kuma ta girma ne a karkashin tasirin al'adun saka kaya na kabilar Miao.

A shekarar 2015, Shu Qiuhong ta bar garinsu ta zo karatu a Jami'ar horar da malamai masu koyarwa ta Shandong. A yayin da take shiga ayyukan kulab din makarantar, a karo na farko ta fara haduwa da rigar Han, kana rigar Han ta ja hankalin ta matuka, har ta mayar da rigar ta zama sana'arta.

Ta ce, "ban yi tsammanin akwai kyawawan tufafi irin wannan ba, idan yarinya ta sanya rigar, za a iya ganin cikakken yanayin tufafin na tausasawa, da laushi na gargajiya a fili".

Da ta waiwayi lokacin da ta shiga kulob din rigar Han a jami'a, Shu Qiuhong ta yi amfani da jimlar "kauna a farkon gani" don bayyana yadda take son rigar Han. Ta ce, "rigar Han tana nuna kyawun mata na gargajiya a bayyane, kuma na fada cikin irin al’adun nan da nan."

Da farko, domin sanya sabbin rigunan Han da sabbin kayan ado a kowace rana, Shu Qiuhong ta fara karanta, da binciken dimbin litattafai da takardu, sannan ta soma koyon yadda ake yin rigar Han da kayan ado.

Bayan zurfafa bincike, ba wai kawai kyawun rigar Han ce ke burge ta ba, har ma ta fi nuna sha’awa kan ma'anar al'adun da irin tufafin gargajiya ke hade da su.

Shu Qiuhong ta ce, "Masu sha’awar rigar Han suna yaba min, da fil din gashi masu salon fulawa iri daban daban da nake yi, ta yadda aka karfafa min kwarin gwiwa wajen kara samun fasahohi, da kara yin sabbin kayan ado masu yawa.”

Shu Qiuhong ta kuma ce, tana yawan musayar al'adun rigar Han tare da masu sha’awarta, kuma ta kan more jin dadi tare da su da irin al’adun ke kawo musu.

Baya ga haka, Shu Qiuhong ta kuma taba bude wani kantin yanar gizo a yayin da take karatu a jami'a, domin sayar da fil din gashi, da rawanin gashi, da dai sauransu, ta yadda ta samu damar mu’amala da mutanen da suke da sha'awar bai daya da ita.

Shekaru uku ko hudu da suka gabata, yayin da Shu Qiuhong ke tafiya kan titi sanye da rigar Han, a wasu lokutan mutane suka cika da mamaki daga rigar ta, wasu su kan yi tsamanin tana sanye ne da rigunan gargajiya na kasar Japan, ko kuma Koriya ta kudu, yayin da wasu ke zaton tana sanye da riga ta daban ne da nufin jawo hankulan mutane kawai.

Shu Qiuhong ta ce, a lokacin, ta kuduri aniyar yin iyakacin kokarinta don ganin ta canza ra’ayin mutanen game da rigar Han.

Bayan ta kammala karatunta a shekarar 2019, Shu Qiuhong ta sami aiki a matsayin malama. A kusan duk lokacin hutu, tana shiga ayyukan da suka shafi al'adun rigar Han, tare da 'yan uwanta masu sha’awar hakan. A lokacin, halinta na kasancewar "Zuciya cike da rigar Han, ba ta da niyyar yin sauran abubuwa".

Domin mayar da hankali kan cimma "Mafarkin rigar Han", Shu Qiuhong ta yi murabus daga aikin koyarwa, kuma ta dukufa wajen fara kasuwanci a birnin na Ji’nan. Irin wannan mataki mai kawo cece-kuce ya taba ruda danginta, har ma suka daina ba ta kudin gudanar da rayuwa. Amma, wannan bai hana ta ci gaba da sana’arta ba, ta rika cin taliya sau daya kadai a ko wace rana. A karshe dai, ta dage kan sana’ar ta bisa karfin zuciyar ta.

Shu Qiuhong ta ce, "A wancan lokacin, iyalina suna adawa da sana’ar da nake yi sosai, har ma mahaifiyata ta yanke hanyar samun kudin shiga na. A wani lokaci mafi muni, sai da ya zama ba ni da komai sai yuan biyu a wuri na." Matsalolin da ta samu a farkon fara raya sana’a, ba su murkushe Shu Qiuhong ba. A watan Satumba na wannan shekarar, Shu Qiuhong da abokiyarta, sun bude wani shago a birnin Ji’nan, domin sayar da rigunan Han da wasu kayan aikin hannu.