Burkina Faso: An rantsar da Ibrahim Traore a matsayin shugaban kasar Burkina Faso na rikon kwarya
2022-10-22 11:34:11 CMG Hausa
A jiya Juma’a ne aka rantsar da Kaftin Ibrahim Traore, a matsayin shugaban kasar Burkina Faso na rikon kwarya, a gaban ‘yan majalissar kundin mulkin kasar a birnin Ouagadougou fadar mulkin kasar.
An amince da nada kaftin Traore a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya ne, yayin zaman majalissar dokokin kasar a makon da ya gabata, ya kuma sanya hannu kan sabon kudurin gwamnatin rikon kwarya, wanda a karkashin sa gwamnatin rikon kwaryar za ta kunshi firaminista, da ministoci da ba za su dara 25 ba, tare da ‘yan majalissar dokoki na rikon kwarya 71.
Juyin mulkin Burkina Faso da kaftin Traore ya jagoranta, shi ne na biyu a cikin wannan shekara, bayan wanda ya kawo karshen gwamnatin shugaba Roch Marc Christian Kabore a ranar 24 ga watan Janairun. (Saminu Alhassan)