logo

HAUSA

Juncao, ciyawar da ke rungumar makomar dan Adam ta bai daya

2022-10-22 22:03:58 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

Jama’a, ko kun taba jin sunan Juncao? Wannan wata nau’in ciyawa ce da ake iya amfani da ita wurin noman laimar kwado da ake iya mai da ita abinci ko magani, wadda ake kiranta “ciyawar kasar Sin” ko “ciyawar samar da arziki” a kasashe da dama.

A shekarun 1980, noman laimar kwado ya zama muhimmin aiki da manoma ke dogara a kai wajen saukaka fatara a lardin Fujian da ke kudu maso gabashin kasar Sin. Sai dai hakan ya haifar da matsala a sakamakon yadda manoma suke yawan saran bishiyoyi don yin amfani da su wajen noman laimar kwado. Ganin haka ya sa Mr. Lin Zhanxi, kwararren masanin ilmin noma da dazuzzuka na kasar Sin, da abokan aikinsa, suka yi kokarin nazari tare da gano fasahar noman laimar kwado ta amfani da nau’in ciyayin Juncao a maimakon katako, a wani kokari na daidaita matsalar. Ta hakan, yawan dazuzzukan da ake sara domin noman laimar kwado ya ragu da yawan gaske. Baya ga haka, sakamakon yadda ciyayin Juncao suka kasance masu iya jure yanayi mai wahala, wadanda kuma suke da saiwoyi masu karfi, baya ga kuma yadda suka kasance masu gina jiki, ya sa bayan noman laimar kwado, ana kuma amfani da su wajen magance iska, da kwararowar hamada, da kuma kiwon dabbobi, wato ke nan, ciyayin na iya taka muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki da kuma kiyaye muhalli duka.

Daga nan, sai Lin Zhanxi ya yayata fasahar zuwa gundumomi 506 na fadin kasar Sin, fasahar da ta taimaka wajen bude kofar samun arziki ga al’umma da ke fama da talauci a kasar. A bara, akwai wani wasan kwaikwayon talabijin da ya yi matukar samun farin jini a kasar Sin, wanda ya bayyana yadda malami Lin Zhanxi ya yayata fasahar Juncao daga Fujian har zuwa yankin Xihaigu na jihar Ningxia, da ke arewa maso yammacin kasar Sin, ta yadda manoman yankin suka saukaka fatara ta hanyar noman laimar kwado.

Malami Lin Zhanxi bai tsaya a gida ba, a maimakon haka, ya kara yayata fasahar zuwa sauran kasashe da shiyyoyin duniya 106. A Lesotho, ya kafa tsarin noma da ke iya samar da laimar kwado da nauyinsu ya kai ton 1.2 a kan fadin kasa da bai wuce muraba’in mita 10 kacal ba, matakin da ya zama muhimmiyar kafar samun karin kudi shiga ga manoman wurin. A kasar Rwanda, kwamitin kula da ayyukan gona na kasar ya yayata fasahar Juncao a sassan kasar wajen kare matsalar lalacewar gonakin kasar. Lallai, ciyayin Juncao sun zama ciyayin samar da arziki da alheri ga al’ummar kasashe masu tasowa da dama.

Daga ranar 16 zuwa 22 ga wata, an gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis dake kan karagar mulkin kasar Sin karo na 20 a birnin Beijing, kuma Malami Lin Zhanxi ma ya halarci taron a matsayin daya daga cikin wakilai 2296 na jam’iyyar. A yayin da yake halartar taron, ya kuma kiyaye tuntuba da abokan aikinsa. Wani lokaci, ya kan kuma tashi da tsakan dare, don yin musayar ra’ayoyi tare da takwarorinsa na kasashen Afirka da Latin Amurka.

Rahoton da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a gun taron na wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, ya yi nuni da cewa, “Kullum kasar Sin na nacewa ga bin manufar diplomasiyya, ta kiyaye zaman lafiyar duniya da tabbatar da samun ci gaban juna, don rungumar makomar dan Adam ta bai daya.” “kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwa da kasashe masu tasowa bisa sahihanci da gaskiya, don kiyaye moriyarsu ta bai daya”. A game da wannan, malami Lin Zhanxi ya bayyana cewa, “Kasar Sin na samar da gudummawar fasahohinta a fannin ayyukan gona ba tare da gindaya wani sharadi ba, kuma muna samar da sahihiyar gudummawarmu, don fatan ganin an saukaka fatara.”

A shekarar 2020, kasar Sin ta cimma nasarar fitar da al’umma kusan miliyan 100 a karkarar kasar Sin daga kangin talauci, kuma kasancewarta kasa mai tasowa mafi girma a duniya, ba ta manta da sauran kasashe masu tasowa ba, har ma ta raba musu fasahohinta ba tare da boye komai ba, don rungumar makomar dan Adam ta bai daya. (Mai Zane: Mustapha Bulama)