logo

HAUSA

Sabon shugabancin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin zai gana da ‘yan jarida a gobe Lahadi

2022-10-22 16:15:54 CMG Hausa

Mambobin zaunannen kwamitin hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) na 20, za su zanta da manema labaru a gobe Lahadi, bayan zaben su a taron da zai gudana goben.

Za a zabi sabbin shugabannin JKS ne a cikakken zama na farko na kwamitin kolin Jam’iyyar na 20, kana za su gana da ‘yan jaridar gida da na waje, da misalin karfe 12 na rana bisa agogon birnin Beijing. (Saminu Alhassan)