logo

HAUSA

An rufe babban taron wakilan JKS na 20 a birnin Beijing

2022-10-22 13:38:39 CMG Hausa

An rufe babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) na 20 da safiyar yau Asabar 22 ga wata, bayan shafe tsawon yini 7 ana yinsa a birnin Beijing, fadar mulkin kasar.

A gun taron, an zabi sabon kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, da sabon kwamitin ladabtarwa da sanya ido na kwamitin kolin, tare da zartas da kuduri game da rahoton kwamitin kolin jam’iyyar JKS karo na 19, da kuduri game da rahoton ayyukan kwamitin ladabtarwa da sanya ido na kwamitin kolin karo na 19, da ma kuduri game da gyararren shiri na kundin ka’idojin jam’iyyar JKS.

Babban taron wakilan jam’iyyar, gami da kwamitin kolinta, su ne hukumar koli ta jam’iyyar. A kan gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar a duk bayan shekaru biyar. (Bilkisu)