logo

HAUSA

Jakadan Sin dake Najeriya ya gana da shugaban jam'iyya mai mulkin kasar Abdullahi Adamu

2022-10-22 15:15:56 CMG Hausa

Kwanan baya, jakadan kasar Sin dake Najeriya Cui Jianchun, ya gana da shugaban jam’iyyar APC mai mulkin kasar Sanata Abdullahi Adamu.

A yayin ganawar, Cui Jianchun ya bayyana cewa, babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, wani muhimmin lamari ne a tarihin harkokin siyasar jam'iyyar da jama'ar kasar Sin. A cikin shekaru 10 da suka gabata, karkashin jagorancin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kasar Sin ta cimma nasarar gina al'umma mai matsakaicin wadata daga dukkan fannoni, kuma ta samu sakamako mai kyau wajen kawar da talauci, da yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata, da yaki da annobar COVID-19 da dai sauransu.

Ya ce jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana son zurfafa musanyar fasahohin da ta samu a harkokin mulkin kasa tare da jam'iyyar APC, da sa kaimi ga hakikanin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, da kiyaye daidaito da adalci a duniya tare, da hada karfi don gina al’umma mai kyakkyawar makoma ga Sin da Afirka a cikin sabon zamani.

A nasa bangaren, Sanata Abdullahi Adamu ya taya murnar gudanar da babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 cikin nasara, ya kuma yaba wa mu'amalar dake tsakanin jam'iyyun biyu, da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, ya kuma jaddada cewa, kasarsa tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak a duniya.

Baya ga haka, ya bayyana aniyarsa ta kara koyo daga fasahohin da jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta samu wajen cimma nasara, da tabbatar da sabon ra'ayin bai daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da inganta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu a fannoni daban daban, don ci gaba da samun sabbin nasarori, ta yadda jama'ar kasashen biyu za su amfana. (Mai fassara: Bilkisu Xin)