logo

HAUSA

Wani lambu mai yanayi na musamman dake birnin Beijing

2022-10-21 15:39:59 CMG Hausa

A cikin shirin yau, za mu ziyarci wani lambun shakatawa mai yanayi na musamman dake nan birnin Beijing na kasar Sin. Wannan lambun shakatawa mai suna Yalugu ya shahara a fannin nuna dimbin abubuwa masu alaka da al’adun wasu kabilun dake lardin Yunnan na kasar Sin. Ban da wannan kuma ana baje kolin itatuwa da bishiyoyi iri daban daban a cikin lambun, wadanda aka fi ganinsu a wasu wurare masu zafi na duniya. (Bello Wang)