logo

HAUSA

Gasar cin kofin duniya ta 2022“Ba a san maci tuwo ba”in ji tsohon dan kwallon Jamus

2022-10-21 15:56:18 CRI

Tsohon mai tsaron baya na kungiyar kwallon kafar Jamus Philipp Lahm, ya ce ba wanda kai tsaye, zai iya bayyana kungiyar da za ta lashe gasar cin kofin duniya na hukumar FIFA, da za a buga nan gaba cikin watan Nuwamba a kasar Qatar, kusan dai nasarar lashe kofin na bana, tamkar karin maganar Bahaushe ne dake cewa “Ba a san maci tuwo ba sai miya ta kare”.

Philipp Lahm mai shekaru 38 da haihuwa, na cikin ‘yan wasan tawagar Jamus da ta lashe kofin na duniya a shekarar 2014 a Jamus. Ya kuma bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, "Abu ne mai wuya a iya fayyace kungiyar turai da za ta iya lashe kofin na bana, duba da yadda akasarin kungiyoyin kasashen na turai ke fama da matsaloli daban daban.

Sai dai duk da haka, Lahm ya ce ko shakka ba bu kungiyoyin turai da na kudancin Amurka kamar Brazil da Argentina, za su yi iyakacin kokarin su domin kare tarihin da suka kafa a baya a wannan gasa. Ya ce “Idan ana batun kare kambi, ina da tabbas game da irin kwazon da za su yi” In ji Lahm.

Ya ce duk da kyakkyawan sakamako da suka cimma yayin wasannin samun gurbin buga gasar ta bana, ba bu tabbas game da irin rawar da kasashen Brazil da Argentina masu kofin na FIFA biyar-biyar za su taka, yayin da suka hadu da sauran kungiyoyi kasashen turai.

A matsayin sa na dan wasan da ya lashe gasar zakarun turai tare da kungiyar Bayern Munich a shekarar 2013, Lahm ya ce kungiyoyin Brazil da Argentina sun nuna kwazo, a wasannin neman gurbin buga gasar cin kofin duniya, amma gasar cin kofin duniya na bukatar karin kwazo da kwarewa.

Game da kasashen Asiya kuwa, Lahm ya ce zai zuba ido don ganin yadda za su nuna bajimtar su a wannan babbar gasa. Ya ce “Gasar cin kofin duniya tamkar gudun yada-kanin-wani ce, dole kungiya ta buga wasanni masu kyau sau sama da 7, ciki har da na kunnen doki domin cimma nasara"

Tsohon dan wasan, wanda kuma ke rike da mukamin daraktan gudanarwa na gasar cin kofin turai na UEFA Euro 2024, wadda Jamus za ta karbi bakunci, ya ce aikin dake gaban duk wata kungiya da za ta fafata a wannan gasa ta cin kofin duniya, shi ne daidaita tsakanin kai farmakin cin kwallaye da tsaron gida.

Ya ce sakamakon da aka gani yayin gasar cin kofin zakarun kasashen turai ko “Nations League” ya tabbatar da hakan. Ya ce an ga yadda manyan kungiyoyi ke shan wahalar gaske a hannun kananan kulaflika, idan suka fuskanci rashin nasara da farko-farkon wasannin su.

Lahm ya ce, irin wadannan kananan kungiyoyi da ake renawa suna da shiri mai kyau idan ana batun kare gida. Ana ma iya cewa, gibin dake tsakanin su da sauran manyan kungiyoyi na kara raguwa sosai.

Wani abun lura ma a cewar Lahm shi ne, karancin lokacin shirin tunkarar wannan babbar gasa ta bana, wanda ya ce na iya zama babban kalubale ga kungiyoyin da za su fafata.

Philipp Lahm, ya kara da cewa, kulaflikan nahiyar turai na iya samun karin fifiko kan saura, saboda wasanni da dama da suke bugawa karkashin gasar zakarun turai ta “Champions League”. Wannan ne fifiko daya da suke da shi sama da takwarorin su na nahiyar kudancin Amurka. Tabbas lashe gasar cin kofin duniya na da nasaba da lashe wasanni da yawa cikin kwanaki kadan a jere.

Tsohon dan wasan na Jamus ya kara da cewa, idan kungiya na da burin lashe babbar gasa, ya zama wajibi kocin ta ya tantance rawar da ko wane dan wasa zai taka. Akwai bukatar tsara yanayin aiki da matakai daban daban, duba da yadda ake bukatar jagororin kungiya su baiwa sauran ‘yan wasa shugabancin da ya dace.

Ya ce ga misali, kungiyar kasar Faransa na daga cikin mafiya karfi a bana, saboda kwarewar daidaikun ‘yan wasan ta, amma idan an zo batun buga babbar gasa irin wannan, dole ne a yi tsari na hade gudummawar jimillar tawagar kasar.