logo

HAUSA

Jihar Anambra ta Nijeriya ta yi gargadi game da barkewer cutar Kwalara

2022-10-21 10:26:25 CMG Hausa

Hukumomi a jihar Anambra dake kudancin Nijeriya, sun bayyana damuwa game da yuwuwar barkewar cutar kwalara da sauran cututtuka masu yaduwa, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da aka samu a yankin, a baya bayan nan.

Da take jawabi yayin wani taron manema labarai jiya a Awka, babban birnin jihar, Chioma Ezenyimulu, shugabar hukumar kula da lafiya a matakin farko ta jihar, ta ce ambaliyar da aka samu a 7 daga cikin yankunan kananan hukumomi 21 na jihar, ta kara haifar da fargabar yuwuwar barkewar cutar kwalara da sauran cututtuka a jihar. (Fa’iza Mustapha)