logo

HAUSA

An kira taron manema labarai na taron wakilan JKS na 20 kan gina kasar Sin mai kyan gani

2022-10-21 15:58:34 CMG Hausa

Cibiyyar ’yan jaridu ta babban taron wakilan JKS karo na 20, ta shirya taron manema labarai karo na biyar Jumma’ar nan a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, inda aka yiwa ’yan jaridun karin haske kan yadda kasar Sin take kare muhalli da halittu.

Mamban rukunin shugabannin JKS, kana mataimakin ministan kula da muhalli da yanayi na kasar Sin, Zhai Qing, shi ne ya jagoranci taron manema labaran wanda ya mayar da hankali kan jigon “Gina kasar Sin mai kyan gani, inda dan-Adam da muhalli za su zauna cikin jituwa.” (Ibrahim Yaya)