logo

HAUSA

Xi Jinping ya jagoranci taron rukunin shugabanni karo na 3 na babban taron wakilan jam’iyyar JKS karo na 20

2022-10-21 15:49:14 CMG HAUSA

 

Yau Juma’a da safe, babban darektan jam’iyyar JKS Xi Jinping ya jagoranci taron rukunin shugabanni karo na 3 na babban taro karo na 20 na wakilan jam’iyyar JKS a babban dakin taron jama’ar kasar Sin, inda aka zartas da daftarin sunayen mambobin kwamitin koli karo na 20 da na mambobi masu jiran gado da daftarin sunayen mambobin hukumar kolin ladabtarwa, wadanda mambobin tawagogin wakilai daban-daban za su tattauna da su. (Amina Xu)