logo

HAUSA

Taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar na 20 da muhimmancinsa

2022-10-21 21:07:06 CMG Hausa

A ranar Lahadi 16 ga watan Oktoba ne aka bude taron wakilai karo na 20 na jam’iyyar kwaminis da ke kan karagar mulkin kasar Sin (JKS) a Beijing, babban birnin kasar Sin, taron dake da muhimmancin gaske, wanda har ya jawo hankalin kasa da kasa. A wannan karon dai an samu halartar wakilai, gami da wadanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300.

Babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban kasar ta Sin, Xi Jinping ya bayyana yayin bude taron cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu wasu manyan nasarori 3 masu matukar muhimmanci, wandada suka shiga tarihin JKS da al’ummar kasar. “Mun cika shekaru 100 da kafuwar JKS, gami da mun shiga wani sabon zamani na gurguzu mai sigar kasar Sin, kuma mun fatattaki kangin talauci baki daya, kana mun kammala ginin al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowanne bangare, wato dai, mun cika burinmu na farko a lokacin da muke murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS.”

Hakika, abin da ya jawo hankalina shi ne, yadda aka fitar da dukkanin mutane da ke fama da kangin talauci a karkarar kasar Sin da yawansu ya kai kusan miliyan 100, abin jinjinawa ne, wanda kuma ya bayar da babbar gudummawa wajen kawar da talauci a duk fadin duniya.

Ta fannin tattalin arziki kuwa an samu haurawar tattalin arziki kakkarfa a shekaru goman da suka wuce. Ma’aunin GDP na kasar a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping a inuwar JKS ya nuna ma’aunin ya karu zuwa kudin Sin Yuan triliyan 114 (kimanin dalar Amurka triliyan 17.72), wannan ya dauki kaso 18.5 na tattalin arzikin duniya. Kasar Sin dai ita ce kasa ta biyu mafi girman tattalin arziki a duniya.

 A baya baya kuwa yaki da cutar COVID-19 ita ma gagarumar nasara ce. Abin jinjinawa ne da burgewa a ganin yadda a karkashin jagorancin JKS aka yaki cutar COVID-19. Gwamantin kasar karkashin shugabancin Xi Jinping ta bayar da duk abin da ya kamata domin ganin an kawar da cutar kamar: kayan gwaje-gwaje da magunguna da gina asibitocin gaggawa da kandagarki a duk fadin kasar. In dai akwai jagoranci na-gari to za’a samu nasara a duk abin da aka yi niyyar aiwatarwa.

Duk wannan ci gaban, da kasar Sin take samu ba abin mamaki ba ne, domin kuwa wannan ya samo asali ne daga jagoranci mai inganci da JKS take bayarwa musamman daga shekarar 1949 da aka kafa jamhuriyar jama’ar Sin da kuma daga shekarar 1978 lokacin da aka fara yin kwaskwarima a gida da kuma bude kofa ga ketare, da kuma nasarorin da aka samu a shekaru goman da suka wuce. (Lawal Sale)