logo

HAUSA

Aikin hada-hadar kudi mai inganci da ci gaban kamfanoni masu jarin gwamnati za su taimaka wajen zamanintar da kasar Sin

2022-10-21 13:39:17 CMG HAUSA

 

A yammacin jiya ne, aka kira taron manema labarai karo na 5 na babban taro karo na 20 na wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda mataimakin gwamnan babban bankin Sin, Pan Gongsheng ya gabatar da manyan nasarorin da aka cimma a fannin hada-hadar kudi cikin shekaru 10 da suka gabata.

Rahoton da Xi Jinping ya bayar a yayin bikin bude babban taro karo na 20 na wakilan jam’iyyar ya bayyana muhimmancin gaggauta kafa sabon tsarin raya kasa, da kara karfin ingiza samun bunkasuwa mai inganci. Game da wannan, Pan ya ce, dole ne a yi kokarin ganin yadda aikin hada-hadar kudi ya taimaka wajen bunkasa tattalin arziki na hadaka, da daidaita samun bunkasuwa da tsaro, da kuma zurfafa aikin yin kwaskwarima da bude kofa ga waje a wannan fanni.

Shugaban kamfanin wutar lantarki na kasar Qian Zhimin ya bayyana cewa, nan gaba, kamfanoni masu jarin gwamnati za su ba da gudunmawarsu a fannonin yin kirkire-kirkire ta fuskar kimiyya da fasaha, samun ci gaba mai inganci, da kara hadin kan kasa da kasa da sauransu. (Amina Xu)