logo

HAUSA

An bukaci kasashen Afirka da su kulla alaka tsakanin raya masana’antu da AFCFTA

2022-10-21 10:24:49 CMG Hausa

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), ta yi kira ga kasashen Afirka, da su karfafa yarjejeniyar yankin cinikayya cikin ’yanci ta nahiyar Afirka ko AfCFTA a takaice, da shirin nahiyar na raya masana’antu, a kokarin ganin an cimma muhimman burin bunkasa nahiyar yadda ya kamata.

Kungiyar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, ciyar da yarjejeniyar ta AfCFTA da bunkasa masana’antun nahiyar kafada da kafada, a kokarin fahimtar juna wajen karfafa cudanya tsakanin bangarorin biyu, zai kai ga samun nasarar muhimmin ginshikin da Afirka ta sanya a gaba, da ma yanayin ajandar raya nahiyar nan da shekarar 2063.

Wannan sanarwa na zuwa ne, gabanin taron manyan jami’an kungiyar game da raya masana’antu, mai taken taron kolin kungiyar Tarayyar Afirka game da masana’antu da rabe-raben tattalin arziki, da zai gudana daga ranar 20 zuwa 25 ga watan Nuwamba a Yamai, babban birnin Jamhuriyar Nijar. (Ibrahim Yaya)