logo

HAUSA

Sin na tallafawa kasashen kungiyar BRICS wajen fadada adadin mambobin kungiyar

2022-10-20 20:30:56 CMG Hausa

A baya bayan nan, Shugaban Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa, ya ce yarima mai jiran gado na masarautar Saudiyya, ya bayyana fatan kasar Saudiyya na shiga kungiyar BRICS.

Game da hakan, a yau Alhamis, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya ce a matsayinta na jagorar kungiyar BRICS a bana, kasar Sin za ta tallafawa kasashen kungiyar BRICS, wajen aza harsashin su na fadada yawan mambobin kungiyar, da kara inganta hadin gwiwar kasashen kungiyar.

Wang Wenbin, ya ce bayan shekaru 16 ana raya ta, hadin gwiwar kungiyar BRICS ya haifar da manyan nasarori, tare da samar da muhimmiyar gudummawa a fannin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. Sakamakon hakan, salon gudanarwar BRICS ya samu yabo da goyon bayan sassan kasa da kasa. Kaza lika, karin kasashen duniya na fatan zama mambobin kungiyar ta BRICS, domin yin aiki tare, don shawo kan wahalhalu da kalubale, tare da cimma moriyar bai daya da wadata.(Saminu Alhassan)