logo

HAUSA

Ainihin ma’anar farfado da kasar Sin a sabon zamani

2022-10-20 19:05:20 CMG Hausa

Ga duk mai bibiyar yadda babban taron wakilan JKS na 20 ke gudana, ba zai gaza jin jimlar “farfado da kasar Sin daga dukkanin fannoni a sabon zamani da ake ciki” ba, musamman cikin rahoton da shugaban kasar, kuma babban sakataren kwamitin kolin JKS Xi Jinping ya gabatar, wanda hakan buri ne na raya kasar da JKS ta sha alwashin cimmawa.

A karkashin wannan manufa, akwai muhimman matakai masu dacewa da salon gurguzu mai sigar musamman da kasar Sin ke bi, wanda ya tanadi samarwa al’ummar Sinawa yanayin rayuwa mai cike da zaman lafiya da wadata, da zamanantar da tattalin arziki da zamantakewa, da bunkasa al’adu, da kyautata alakar rayuwa tsakanin bil adama da sauran halittu, wadanda sakamakon su zai amfani dukkanin sassan al’ummun kasar ba wai wasu mutane kalilan ba.

Idan muka kalli wannan salon samar da ci gaba na kasar Sin, za mu ga ya sha banban da na kasashen yamma masu bin salon jari-hujja, wadanda tarihi ya jima da sanin su, a matsayin masu amfani da karfin tuwo, da mulkin mallaka wajen fadada tasirinsu a duniya, da cimma muradun kashin kai ta kowace irin hanya.

Ko shakka babu, salon gurguzu mai halayyar musamman na Sin, ya haifar da babbar dama ta yakar talauci, inda karkashinsa kasar ta cimma nasarar tsamo al’ummarta da yawansu ya kusa miliyan 100 daga kangin talauci cikin shekaru 10 kacal, matakin da masu fashin baki ke ganin ya shiga tarihin duniya, a matsayin irin wanda ba a taba gani ba a shekarun baya bayan nan.

Alal hakika, JKS ta dora muhimmancin gaske ga moriyar al’ummar Sinawa. Jam’iyya ce da har kullum ke aiki tukuru, wajen ganin ba a bar wani rukuni na al’umma a baya ba a dukkanin fannonin ci gaba. Ana kuma iya ganin hakan a zahiri, idan aka yi duba ga bangarorin da kasar Sin ta cimma manyan nasarori a cikinsu, kamar bunkasar tattalin arziki, da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, da fadadar fannin ilimin kimiyya da fasaha, da karuwar guraben ayyukan yi, da tsara manufofin inganta rayuwar tsofaffi da yara kanana da sauran su. Tabbas wannan kadan ne daga ainihin ma’anar matakan farfado da kasar Sin a sabon zamani.(Saminu)