UNICEF: Kaso 36 na yara ne ke fara karatu da wuri a Nijeriya
2022-10-20 10:59:39 CMG Hausa
Asusun kula da kananan yara na MDD, ya ce 1 cikin yara 3 a Nijeriya, ko kaso 36 na yaran ne ke fara karatu da wuri, inda ya yi kira da a kara adadin a kasar mafi yawan al’umma a nahiyar Afrika.
Yetunde Oluwatosin, kwararriya kan harkar ilimi na asusun UNICEF a Nijeriya, ta shaidawa manema labarai yayin wani taron tattaunawa na yini biyu a jihar Sokoto dake arewa maso yammacn kasar cewa, adadin yaran dake fara karatu da wuri, abun damuwa ne, inda alkaluma suka nuna wagegen gibin dake tsakanin yaran masu kudi da na marasa shi.
Jami’ar ta ce lokacin yarinta muhimmi ne da ya kamata kowacce kasa ta mayar da hankali kai, bisa tunanin cewa, hakan zai inganta rayuwar yara. Tana mai cewa, dole ne a gina wannan lokaci domin bayar da gudunmuwa wajen sauya rayuwar yara tun da wuri. (Fa’iza Mustapha)