logo

HAUSA

Sassa daban daban na kasar Sin sun sa niyyar kara bude kofarsu ga ketare

2022-10-20 15:05:47 CMG Hausa

An ambaci kalmomin “Bude Kofa” sau da dama, a cikin rahoton da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a yayin bikin bude babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20. Rahoton ya bayyana cewa, za a inganta aikin bude kofa ga ketare cikin babban mataki, da kyautata manufofi da tsare-tsaren da za su dace da manufar bude kofar, da gaggauta gina kasa mai karfin cinikayya da inganta neman ci gaba tare bisa shawarar “ziri daya da hanya daya”, da kuma kiyaye mabanbantan tsare-tsaren tattalin arziki da dangantakar tattalin arziki da cinikayya na duniya cikin kwanciyar hankali.

A yayin taron manema labaru karo na uku da aka gudanar a cibiyar yada labaru na babban taron a jiya Laraba, wasu kakakin tawagogin larduna da na jihohi masu zaman kansu, sun bayyana cewa, za su kara bude kofar yankunansu ga ketare, ta yadda za a iya kara dacewa da sabon tsarin neman ci gaba na kasar.

A cikin rahoton, shugaba Xi ya bayyana cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta yi yakini sosai ta dauki dimbin matakan bude kofa ga ketare, sannan gabatar da shawarar “ziri daya da hanya daya”, har yanzu su kasance tamkar wata haja ko dandalin hadin gwiwar kasa da kasa da suke samun karbuwa a duk fadin duniya, Bugu da kari, kasar Sin ta zama babbar abokiyar cinikayya ta kasashe da yankunan duniya fiye da 140. jimilar kayayyakin cinikayya a tsakanin kasar Sin da sauran sassan duniya ta kai matsayi na farko a duniya. Yawan jarin waje da baki ’yan kasuwa suka zuba a kasar Sin, ko ‘’yan kasuwar kasar Sin suka zuba a ketare, dukkansu suna sahun gaba a duniya. Hakan ya alamta cewa, kasar Sin ta riga ta kafa wani yanayin kara bude kofarta ga ketare a karin fannoni daban daban ta hanyar kara gyara fuskokin dokoki da dai makamatansu. (Safiyah Ma)