logo

HAUSA

Sheriff Ghali Ibrahim: Tsarin gurguzu mai sigar kasar Sin a sabon zamani da yadda kasar ta tsara burikan ci gaba za su taimaka ga bunkasar kasar

2022-10-19 15:57:29 CMG Hausa

A halin yanzu ana ci gaba da gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS karo na 20 a Beijing, kuma a cikin muhimmin rahoton da shugaba Xi Jinping ya gabatar a yayin bude taron, ya zayyana manyan nasarorin da kasar ta samu a shekarun baya, da tsara burikan samar da ci gaban kasa a shekarun dake tafe, al’amarin da ya shata alkibla ga bunkasar kasar Sin nan gaba.

Farfesa Sheriff Ghali Ibrahim, shi ne darektan cibiyar horas da ’yan majalisu na jami’ar Abuja, kana masanin harkokin kasar Sin a tarayyar Najeriya. Ya yi fashin baki kan wasu abubuwan da suka burge shi a cikin rahoton Xi. (Murtala Zhang)