Matakan kasar Sin na bude kofa za su amfanawa sauran sassan duniya, ciki har da kasashen Afirka
2022-10-19 09:45:57 CMG Hausa
Tun lokacin da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar zurfafa gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen ketare, kasar take samun manyan nasarori a fannoni daban-daban. Wannan ya sa ta kara nanata kudurinta na inganta hadin gwiwa da sauran kasashe a fannin kimiyya da fasaha da kirkire-kirkire tare da fadada bude kofa ga kasashen ketare.
Alkaluman ci gaban kirkire-kirkire na kasa da kasa na shekarar 2022 da hukumar kare ikon mallakar fasaha ta duniya (WIPO) ta fitar sun nuna cewa, kasar Sin ta zo ta 11 a kididigar kirkire-kirkire ta duniya, karuwar mataki daya kan na shekarar da ta gabata.
Wannan ya sake tabbatar da manyan nasarorin da kasar ta samu a fannin kare ikon mallakar fasaha. Kasar Sin tana dora muhimmanci matuka kan kirkire-kirkire na kimiyya da fasaha da cudanya a fannin sadarwar zamani ta duniya, da kare ikon mallakar fasaha yadda ya kamata, da karfafa hadin gwiwar kasa da kasa kan kirkire-kirkire da kimiyya da fasaha a dukkan fannoni.
Haka kuma alakar Sin da kasashen Afira, musamman Najeriya dake zama kasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, ta haifar da kyakkyawan sakamako a fannoni da dama, kamar layukan dogo tsakanin Abuja da Kaduna, kuma tsakaninLagos da Ibadan, da tashar samar da wutar lantarki mai amfani da karfin ruwa da gyara makarantu da cibiyar koyon Sinanci a karamar sakandare dake yankin Garki II, a Abuja da kamfanonin kasar Sin suka gudanar da dai sauransu. Baya ga fannonin na sadarwa da masana’antu da zuba jari da harkokin cinikayya da su ma wannan hadin gwiwa ta shafa.
Kasashen Kenya da Rwanda da Habasha da Tanzaniya da sauransu, na daga cikin kasashen Afirka da suka amfana da alakarsu da kasar Sin, kama daga layukan dogo da tagwayen hanyoyin mota na zamani da samar da hidimar jinya da magunguna da horo ga ma’aikatan lafiya da makamantansu. A takaice dai alakar Sin da Afirka da kuma Sin da Najeriya, hadin gwiwa ce ta moriyar juna da mutunta juna, dake zama Mahdi ka ture. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)