logo

HAUSA

Xu Ganlu: Sin na cikin kasashe mafiya tsaro

2022-10-19 21:07:41 CMG Hausa

Mataimakin ministan ma’aikatar tsaron al’umma ta kasar Sin Xu Ganlu ya ce sassan duniya daban daban sun yi imani da kyakkyawan yanayin tsaron kasar Sin.

Xu Ganlu, wanda ya bayyana hakan a yau Laraba, yayin taron manema labarai, a gefen babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin(JKS) na 20, ya ce Sin na cikin kasashe da ake samun karancin laifin kisan kai, da laifuka masu alaka da harbin bindiga da ababen fashewa. Kaza lika kasar ta samu matukar raguwar laifuka, da karancin hadurra cikin shekaru 10 da suka gabata.

Jami’in ya kara da cewa, a shekarar 2021, adadin manyan laifuka sun ragu da kaso 64.4 bisa dari kasa kan na shekarar 2012, yayin da laifuka masu nasaba da ta’ammali da miyagun kwayoyi suka ragu da kaso 56.8 bisa dari, kana laifuka masu alaka da fashi da makami suka ragu da kaso 96.1 bisa dari, kuma na sace-sace sun ragu da kaso 62.6 bisa dari cikin wannan wa’adi.

Alkaluman jin ra’ayin al’umma da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a shekarar 2021, sun nuna yadda kaso 98.6 bisa dari na wadanda aka zanta da su suka bayyana gamsuwa bisa kyakkyawan yanayin tsaron rayukan su a kasar Sin, alkaluman da suka karu da kaso 11 bisa dari idan an kwatanta da na shekarar 2012.  (Saminu Alhassan)