logo

HAUSA

Kasar Sin tana aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tsarin dimokuradiyya

2022-10-19 14:40:24 CMG Hausa

A yayin da babban sakataren jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) ke gabatar da rahoto a lokacin bude taron wakilan jam’iyyar karo na 20, da ya gudana ranar Lahadin da ta gabata, ya yi cikakken bayani kan halayyar musamman game da manufar aiwatar da dukkan ayyukan gwamantin Sin bisa tsarin dimokuradiyya, gami da fifikon manufar. Hakan, ya nuna yadda za a aiwatar da harkokin kasar bisa tsarin dimokuradiyya na gurguzu, da yadda kasashe daban-daban za su fahimci ingancin tsarin dimokuradiyyar Sin.

Manufar aiwatar da dukkan ayyukan gwamnati bisa tsarin dimokuradiyya ta kunshi bangarorin gudanar da zabe, da tattaunawa da tsai da kuduri game da matakan gwamnati, da kulawa da sa ido kan harkokin kasar, duk karkashin tsari na dimokuradiyya, ta yadda za a fahimci bukatun jama’a a fannonin harkokin siyasa da zaman al’umma.

Tsarin dimokuradiyya tsakanin kasashe ya sha bamban. Idan har tsari ya dace da yanayin da kasar ke ciki, to, zai amfani al’ummar kasar. JKS za ta ci gaba da kokarin aiwatar da manufar tafiyar da dukkan ayyuka bisa tsarin dimokuradiyya, don tabbatar da jama’a a matsayin jigon kasa, gami da samar da gudunmowa ga aikin inganta tsare-tsaren siyasa dake shafar muradun bil-Adam. (Bello Wang)