logo

HAUSA

MDD ta kara samar da tallafi a kasar Chadi yayin da ambaliyar ruwa ta shafi mutane miliyan 1

2022-10-19 10:27:13 CMG HAUSA

 

Stephane Dujarric, babban mai magana da yawun magatakardan MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, MDD da abokan hulda dake samar da agajin jin kai, suna kara kokarin samar da agaji ga sama da mutane miliyan 1 da ambaliyar ruwa ta shafa a kasar.

Dujarric ya bayyana cewa, ambaliyar ta fi shafar yankin kudancin kasar, da ma wasu larduna dake gabashin kasar, kamar Sila, inda ta sanya koguna tumbatsa. Ambaliyar ta shafi larduna 18 cikin larduna 23 na kasar dake yankin Sahel.

Ya kara da cewa, ruwan dake toroko ya mamaye unguwannin birnin N’Djamena, lamarin da ya tilastawa mutane kaurewa matsugunansu. Bayanai na cewa, kimanin hekta dubu 465 na gonaki ne suka lalace, lamarin da ya kara ta’azzara matsalar karancin abinci da kasar ke fuskanta. (Ibrahim Yaya)