logo

HAUSA

Sin za ta karfafa kariya ga ikon mallakar fasaha, in ji wata babbar mai shari’a

2022-10-19 21:09:55 CMG Hausa

Mataimakiyar shugaban kotun kolin al’ummar kasar Sin He Rong, ta ce sassan hukumomin shari’ar kasar Sin za su kara azamar karfafa kariya ga ikon mallakar fasaha ko IPR, a wani mataki na tallafawa kasar Sin wajen cimma dogaro da kai, da karfafa ilmomin kimiyya da fasaha.

Mai shari’a He Rong ta bayyana hakan ne a Larabar nan, yayin taron manema labarai da ya gudana a gefen babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (JKS) na 20, ta ce za a samar da dokoki masu karfi na kare ikon mallakar fasahohi, musamman a fannonin da suka jibanci fasahar killace manyan bayanai, da na kwaikwayon tunanin bil adama, da kimiyyar binciken kwayoyin halittun bil adama. Kaza lika za a kyautata aiwatar da matakan shari’a domin dakile babakere da takara maras adalci.   (Saminu Alhassan)