logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Uganda sun taya juna murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashensu

2022-10-18 14:17:24 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Uganda, Yoweri Museveni, sun taya juna murnar cika shekaru 60 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashensu, a yau Talata.

A cewar shugaba Xi Jinping, yana daukar dangantakar kasarsa da Uganda da muhimmanci, kuma a shirye yake ya hada hannu da shugaba Museveni, wajen daukar wannan lokaci a matsayin wata dama ta zurfafa dangantaka a bangarori da dama, karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika, domin moriyar kasashen biyu da al’ummominsu da gina al’ummar Sin da Afrika mai makoma ta bai daya a sabon zamani.

A nasa bangaren, shugaba Museveni ya ce tun bayan kulla huldar diflomasiyya tsakanin kasashen shekaru 60 da suka gabata, Uganda da Sin sun yi aiki tare wajen aiwatar da muhimman ayyukan hadin gwiwa, karkashin kyakkyawar dangantakarsu dake kara karfi.

Ya kara da cewa, bangaren Uganda zai jajirce wajen inganta dangantakarta da Sin, yana mai bayyana kwarin gwiwar abota da hadin gwiwar kasashen biyu za su ci gaba da zurfafa, ta yadda al’ummominsu za su kara amfana, tare da ba da gudunmuwa ga tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hakali da hadin gwiwa a duniya. (Fa’iza Mustapha)