logo

HAUSA

Ana sa ran jirgin saman Nijeriya zai fara aiki kafin karshen shekara

2022-10-18 10:38:40 CMG Hausa

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce jirgin saman Nigeria Air na kasar, ya kai kaso 91 na kammaluwa, kuma ana sa ran kaddamar da shi kafin karshen bana.

Da yake jawabi yayin taron nazarin ayyukan ma’aikatu, jiya Litinin a Abuja babban birnin kasar, shugaba Buhari ya ce an samu karin nasara bayan hukumar kula da sufurin jiragen saman fasinja ta kasar ta bayar da shaidar tabbacin aiki ga filayen jiragen sama na kasa da kasa na Abuja da Lagos, yayin da yanzu haka filayen jiragen sama na Kano da Port Harcourt, ke kokarin samun makamanciyar shaidar. 

Ma’aikatar kula da sufurin jiragen sama ta kasar, ta sanar a watan da ya gabata cewa, jirgin na Nigeria Air, ya fara daukar kwararrun ma’aikata domin fara sufuri. Inda ta kara da cewa, wani kamfani ne zai tafiyar da harkokin jirgin, inda gwamnatin Nijeriya za ta mallaki kaso 5 na hannun jarinsa, yayin da ’yan kasuwa a kasar, za su mallaki kaso 46. Sannan kuma, an ware raguwar kaso 49 ga wasu muhimman abokan hulda, ciki har da baki masu son zuba jari. (Fa’iza Mustapha)