logo

HAUSA

Dakarun kiyaye zaman lafiya na MDD biyu sun mutu, kana hudu sun jikkata a arewa maso gabashin kasar Mali

2022-10-18 10:13:18 CMG Hausa

Tawagar MDD dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Mali ko MINUSMA a takaice, ta wallafa a shafinta na tiwita jiya cewa, dakarunta guda biyu sun gamu da ajalinsu, kana wasu 4 sun jikkata, bayan da motar da suke ciki ta taka wata nakiya a yayin da suke sintiri da aikin bincike a garin Tessalit dake arewa maso gabashin kasar.

Sanarwar wadda shugaban tawagar ta MINUSMA, El-Ghassim Wane ya sanyawa hannu, ta bayyana cewa, “muna jinjinawa dakarun wanzar da zaman lafiyar 2 da suka kwanta dama da kuma hudu da suka jikkata a garin Tessalit, biyo bayan fashewar wata nakiya. Haka kuma bama-bamai na daya daga cikin manyan barazana da abokan aikinmu ke fuskanta. Don haka, ina sake jinjina musu kan yadda suke jajircewa kan ayyukansu.”

A ranar 29 ga watan Yunin shekarar 2022 ne, kwamitin sulhun MDD, ya cimma wani kuduri mai lamba 2640, wanda ya ba da damar tsawaita wa’adin tawagar MINUSMA har zuwa ranar 30 ga watan Yunin shekarar 2023. (Ibrahim Yaya)